BBCHausa.com
Inglishi
Larabci
Faransanci
 
An sabunta: 23 Oktoba, 2009 - An wallafa a 08:56 GMT
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
Ghana Za Ta Binciki Mussababin Gobara
 
Ma'ikatar Kula Da Harkokin Waje Ta Kone Kurmus
Ma'ikatar Kula Da Harkokin Waje Ta Kone Kurmus
Gwamnatin Ghana ta ce za ta gudanar da cikaken bincike don gano abin da ya haddasa wata gobara da ta lashe ginin ma'aikatar harkokin wajen kasar kurmus a Accra babban birnin kasar a ranar labara da dare.

A wata ziyarar gani da ido da ya kai a wajen da safiyar alhamis shugaban kasar wato Farfesa John Atta Mills ya ce ba zai yi aiki da jita jita koko zato ba illa gaskiyar da kanta duk kuwa da zargin da ake yi cewa da hannun wasu a lamarin .

Sai dai babban komandan 'yan sandan lardin Accra wato Rose Tinga Bio ta ce sun cafke wasu mutane uku da ake zargi da hannu a gobarar.

Shugaban kasar ya ce wannan wani babban kalubale ne ga gwamnatin sa, abun da kuma ya ce bai kai ya razanard a al'ummar kasar ba.

Ya ce a halin da ake ciki ba zai dora wa kowa laifi ba, abin da kawai ya ke son gani shine gaskiyar lamarin.

Shugaba John Atta Mills ya yi kira ga ma'aikatan da su kwantar da hankalin su a yayin da gwamnatin ta ke kokarin sake tsugunnar da su.

Shugaban Kasar Ghana Farfesa John Attah Mills
Shugaban Kasar Ghana Farfesa John Attah Mills

Ya ce wannan lamari da ya auku shi ke nuna cewa lallai ma'aikatar kashe gobarar kasar bata cikin shirin tunkarar gobara mai tsanani irin haka, inda ya yi nuni da cewa gwamnatin kasar za ta taimaka mata da kayan aiki.

Alamar Da Gangan

Kwamandar 'yan sandar jihar Accra wato Rose Tinga Bio ta ce akwai alamar dake nuna cewa da gangan aka hasa gobarar.

Ta ce binciken da suka gudanar ya nuna cewar wasu mutane sun shiga cikin ginin ma'aikatar, kuma fitar su daga cikin ginin ke da wuya, sai gobarar ta tashi.

Tace a yanzu haka mutane uku da suka cafke suna amsa tambayoyi.

Wakilin BBC a Ghana Idi Ali yace a lokacin da ya isa wajen dai ya iske bakin hayaki na fitowa daga hawan karshe na ginin mai hawa goma.

Ya ce koda allura ba'a fitar daga cikin ginin ba. Wani cikin 'yan kwana-kwana da ya iske a wajen ya shaida mi shi cewar suna ji suna gani, ginin ya kone kurmus saboda gobarar tafi karfinsu.

Tawirar Ghana
Kasar Ghana Na Fama Da Matsalar Gobara

Binciken da Wakilin BBC ya gudanar ya nuna cewar, a wannan shekarar ma'aikatun gwamnati guda uku kenan gobara tayi wa barna wato da ma'aikatar yada labarai da ta makamashi da kuma ma'aikatar harkokin waje.

A hirar da yayi da wani gidan radio mai zaman kansa dake Accra ministan harkokin wajen kasar wato Alhaji Muhammed Mumuni wanda a yanzu haka ya ke halartar wani taro a kasar Malawi ya ce hakan shike nuna cewa ba banza bane, kamata yayi a bincika.

 
 
KA KUMA DUBA
 
 
Aika ìmel ga aboki   Wanda za a iya gurzawa
 
  Game da mu|Tuntube mu
 
BBC Copyright Logo
 
^^ Koma sama
 
  Labarai | Yanayi
 
  BBC News >> | BBC Sport >> | BBC Weather >> | BBC World Service >> | BBC Languages >>
 
  Taimako | Tuntube mu | Tsare Sirri